Za Mu Hukunta Bankuna Masu Bayar Da Tsoffin Kudi – CBN

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa duk da wa’adin da babban bankin kasa CBN ya dauka na daina amfani da tsoffin kudade na matsowa, bankunan kasar nan ba sa zuwa karbar sabbin kudin da aka buga, a cewar babban bankin.

CBN ya ce ya sha rokon bankunan kasar nan da su zo su dauki sabbin kudaden amma ba sa zuwa gaba daya maimakon haka suna cigaba da ba ‘yan Najeriya tsoffin kuɗin.

A shekarar 2022, CBN ya sanar da yin sabbin kudaden Naira da suka hada N200, N500 da N1,000, sun fara aiki a ranar 15 ga watan Disamba, tsoffi kuma za su yi sallama da amfani a ranar 31 ga watan Janairun bana.

Yayin da har yanzu ake ci gaba da kai ruwa rana game da karbar sabbin kudin, karancin kudin ma na daga cikin abin da mutane suka fi mai da hankali a kai.

Da yake magana a wani taron wayar da kan jama’a game sa sabbin kudi a Legas, shugaban tawagar doka ta CBN a jihar, Kofo Salam-Alada ya ce babban bankin zai tsanantawa bankunan kasuwanci da ke ƙoron sabbin kudin a ATM. Ya bayyana cewa, babban bankin ya shirya daukar matakin kakaba tara da hukunci kan bankunan da ke kin ba kwastomomi sabbin kudi a ATM.

“Zan iya fada muku a yau cewa a kullum CBN na ba da sabbin kudi. Da nake magana daku, bankuna na can a CBN don karbar kudin. “Muna ma rokon Bakunan ne da su zo su dauki kudin daga Babban Bankin. Muna da sabbin kudin nan a ma’ajiyarmu kuma muna rokon bankuna da su zo su dauke su.

“Mun gano akwai abubuwa da yawa da ke faruwa da suke bukatar mu magance, don haka muka hana cire sabbin kudi a kan kanta don tabbatar da kowa zai samu kudin ba wai wani mai kudi da ya san manaja ba, da zai shigo ya debe dukkan sabbin kudin a bankin reshe.

“Wannan ne yasa muka ce kudaden su zauna a ATM wanda ta hakan ba zai bambanta mutane ba.” Salam-Alada ya kuma bayyana cewa, babban bankin na ci gaba da sanya ido kan bankunan domin gano yadda sabbi da tsoffin kudade ke yawo a kasar.

Labarai Makamanta