Za Mu Haɗa Hannu Wajen Kawar Da Ta’addanci A Najeriya – Gumi Da Buru

Malaman addinan na Musulunci da Kiristanci sun bayyana hakan ne a yayin ziyarar barka da Sallah da Pastor Yohanna Buru ya kai wa sanannen malamin addinin Islama Dr. Ahmad Abubakar Mahmoud Gumi a gidanshi dake Kaduna.

Pastor Buru ya bayyana Dr Gumi a matsayin wani ginshiki da ke bada gudunmawa wajen yakar ta’addanci a Najeriya wanda gudummuwar da ya bayar abu ne wanda ba za’a taɓa mantawa ba.

Sannan ya bayyana aniyar shi ta kasancewa da Dr Gumi a kowane lokaci a kokarin da yake yi na sulhu da ‘yan bindiga a sassan arewacin kasar.

Lokacin da ya ke maida jawabi mashahurin Malami Dr Gumi ya godewa Pastor Buru da tawagarshi bisa ga ziyarar da suka kawo mishi, inda ya bayyana muhimmancin haɗa hannun Malaman Addini wuri guda domin daƙile yaɗuwar ta’addanci a tsakanin jama’a.

Labarai Makamanta