Za Mu Dawo Da ‘Yan Najeriya Cikin Hayyacinsu – Shugaban ‘Yan Sanda

Babban Baturen ‘yan Sanda na kasa Usman Baba, ya bada tabbaci ga ‘yan Najeriya na dawo da tsaro cikin kasar inda yace ya ce jami’an tsaro na aiki tukuru wurin tabbatar da cewa sun shawo kan matsalar tsaron kasar nan, komai ya daidaita.

Shugaban ‘Yan sandan wanda ya samu wakilcin DIG Danmallam Mohammed, ya sanar da hakan ne yayin da ake yayen ‘yan sandan da suka samu horo a bangaren shugabanci a kwalejin ‘yan sanda dake Jos babban birnin Jihar Filato.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito, ya ce hukumar ‘yan sanda na aiki tukuru wurin dawo da zaman lafiya a dukkan sassan kasar nan kuma tana hada kai da sauran hukumomin tsaro. “Muna aiki tukuru wurin tabbatar da zaman lafiya tare da daidaituwa ta shawo kan matsalar tsaro a dukkan sassan Najeriya.

“Tsaro al’amari ne ya da shafi kowa, ba zamu iya yin shi mu kadai ba. Muna yin iyakar kokarinmu tare da hada kai da sauran hukumomin tsaro wurin tabbatar da tsaro. “Da izinin Ubangiji tare da taimakon ‘yan Najeriya, za mu shawo kan ta’addanci, ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da dukkan wani nau’i na rashin tsaro a kasar nan.”

Shugaban ‘yan sandan ya sha alwashin horarwas za ta zama wani jigo na mulkinsa saboda hakan ne kawai zai tabbatar da ingancin tsaro a kasar nan.

A yayin nasiha ga wadanda suka samu horon, Baba ya kwatanta zanga-zangar EndSARS da abu mara dadi tare da kira ga jami’an da su sake duba hakkokin dan Adam yayin da zasu fara shugabanci.

Labarai Makamanta