Za Mu Daukaka Kara Kan Hukuncin Kotu – Kungiyar ASUU

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta sha alwashin ɗaukaka ƙara game da hukuncin kotun ɗa’ar ma’aikata, wanda ya umarci Malaman jami’a su koma bakin aiki.

An ruwaito ƙungiyar na cewa tuni ta fara tattara lauyoyi bisa jagorancin sanannen lauya mai fafutukar kare haƙƙin ɗan adam, Femi Falana (SAN), domin shigar da ƙara a gaba.

Shugaban ASUU na shiyyar jihar Legas, Adelaja Odukoya, a wata sanarwa da ya fitar bayan Kotu ta yanke hukunci, ya roki mambobin ƙungiyar su kwantar da hankulansu kuma su ɗaura ɗamarar yaƙi har karshe.

An jiyo shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, a cikin sanarwan yana mai rokon fusatattun lakcarori su kwantar da hankalinsu, babu wani abun damuwa kan umarnin su koma aiki.

“Ya kamata Mambobin mu su kasance a shirye su haɗa kai. Duk mutanen da kansu a haɗe yake babu mai yin nasara a kansu.” inji Osodoke.

Labarai Makamanta