Za Mu Cigaba Da Ba Talakawa Tallafin Dubu 50,000 – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da biyan kudaden tallafi ga gama garin mutane da ‘yan kasuwa a matsayin wani bangare na kokarin ta na rage mummunar tasirin kwayar cutar Corona a kan ‘yan Nijeriya, in ji kakakin fadar gwamnati a ranar Lahadi.

Ana biyan kudaden ne a karkashin shirin gwamnatin na Survival Fund, wani bangare na shirin bunkasa tattalin arziki (ESP).

Kunshin kudi tiriliyan N2.3 na ESP, shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da shi a ranar 24 ga Yuni, 2020.

Kanana da matsakaitan masana’antu (MSME) suna da damar samun tallafin N50,000 a matsayin wani bangare na shirin.

Don raya ayyukan yi, tsarin biyan yana nufin tallafawa kamfanoni 500,000 tare da biyan N50,000 ga kowane ma’aikaci na tsawon watanni uku.

Hakanan ana tallafawa masu sana’ar hannu da masu kasuwancin safara da tallafi na N30,000 na lokaci daya.

A cewar wata sanarwa daga kakakin fadar gwamnati, Laolu Akande, tuni ‘yan Najeriya 319,755 suka ci gajiyar shirin na biyan albashi, yayin da ‘yan Nijeriya 265,425 suka ci gajiyar a karkashin shirin masu sana’ar hannu da masu kasuwancin safara.

Tsarin yana kuma taimaka wa kananan ‘yan kasuwa domin yin rijista tare da Hukumar Kula da Harkokin Kasuwanci (CAC).

Kimanin kamfanoni 172,129 suka ci gajiyar tallafin rijistar kawo yanzu. Manufar ita ce a yi rajistar sabbin kamfanoni 250,000.

An kiyasta shirin tallafin na Korona zai kubutar da ayyuka miliyan 1.3 a fadin kasar kuma ya shafi mutane 35,000 a kowace jiha, a cewar gwamnati.

An fara cike neman tallafin tun ranar 9 ga watan Fabrairu an kuma rufe a ranar 1 ga watan Maris duk a 2021.

Labarai Makamanta