Za Mu Cigaba Da Azabtar Da Yarbawa Da Yunwa – Miyyeti Allah

Shugaban kungiyar Miyetti Allah Association of Cattle Breeders na Kasa reshen jihar Kwara, Aliyu Mohammed ya ce za a cigaba da hana kai abinci zuwa kudu har sai dukkanin wani Bayarabe ya tagaiyara sakamakon cutar da Fulani.

Alhaji Aliyu Mohammed ya ce za a cigaba da tare kayan abinci da su ka nufi yankin kudu ta jihar Kwara, har sai an tabbatar cewa za a tsare ran Fulanin yankin ko kuwa azabar yunwa ta kassara yankin gaba daya.

Mohammed ya bayyana wa manema labarai hakan ne bayan kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta ƙasa sun yi wani muhimmin taro a Ilorin babban birnin jihar Kwara ranar Lahadi.

Shugaban kungiyar ya ce sun dauki wannan mataki ne domin ja-kunnen mutanen Kudu a kan cin-kashin da ake yi wa Fulani da su ke neman na abincinsu a waje.

“Akwai bata-gari a ko ina, kamar yadda ake da bara-gurbi da mutanen kwarai a al’umma.” Saboda haka a daina yi wa Fulani kuɗin Goro da aikin ta’addanci.

“Ba Fulani kadai su ke laifi a kasar nan ba, abin haushi ne ace yanzu duk abin da ya faru sai a zargi makiyaya Fulani.”

MACBAN ta bukaci a kama Sunday Igboho jagoran tsagerun Yarbawa da ya jagoranci kisa akan fulani, sannan Ƙungiyar ta Miyetti Allah ta ce za ta tona asirin duk wani da ya zo jihar Kwara da sunan Fulani, ya na barna.

A jawabin na sa, Aliyu Mohammed ya yaba wa gwamna Abdulrahman Abdulrazaq, ya ce ko kodan, gwamnatinsa ba ta nuna wa Fulani bambanci a jihar Kwara.

Labarai Makamanta

Leave a Reply