Za Mu Bukaci Biliyan 305 Domin Aiwatar Da Zaben 2023 – INEC

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu ya ce hukumar za ta bukaci Naira biliyan 305 domin gudanar da zabukan 2023.

Ya bayyana hakan ne a wata ganawa da kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa a zauren majalisar a ranar Litinin 20 ga watan Disamba, 2021.

Shugaban na INEC ya kuma lura da cewa adadin kudin ne zai baiwa hukumar damar shirya zabe da kuma siyan duk kayan aikin zaben da ake bukata da kuma gudanar da zabukan fidda gwani a fadin kasar nan.

Sai dai ya bayyana cewa tuni hukumar ta karbi Naira biliyan 100 daga cikin kudaden da ake bukata na zaben.

A halin da ake ciki, shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da kasafin kudi Sanata Jibrin Barau, ya bayyana cewa za a gabatar da kasafin kudin shekarar 2022, a yi muhawara, sannan a zartar da shi a ranar Talata 21 ga watan Disamba.

Labarai Makamanta