Za Mu Bude Hanyoyin Sadarwa Kwanan Nan A Zamfara – Matawalle

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnan Bello Mohammed Matawalle, ya sanar da cewa ranar Litinin ko Talata za’a mayar da layukan sadarwa da aka katse a jihar sakamakon matsalar tsaro.

Matawalle ya bayyana hakan ne yayin zaben Shugabannin jam’iyyar All Progressive Congress APC wanda ya gudana a Gusau babban birnin Jihar.

A taron, Gwamnan yace za’a dawo da sabis kuma mutane zasu koma cin kasuwanninsu na mako. Idan an tuna cewa a ranar 4 ga Satumba na wannan shekara an datse sabis domin shawo kan lamarin garkuwa da mutane da ya addabi jihar.

A cewarsa: “A bayanan da muka samu, an samu saukin hare-haren da ake kaiwa garuruwa kuma nan da Litinin ko Talata, kowa a jihar zai iya waya da jama’a.”

Labarai Makamanta