Za A Yi Nadamar Ayyana ‘Yan Bindiga Matsayin ‘Yan Ta’adda – Gumi

Rahotanni dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Fitaccen malamin addinin Islaman nan da ke da’awar yi wa ƴan fashin daji masu satar mutane wa’azi, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi gargadin cewa za a yi da na-sanin ayyanasu a matsayin’ yan ta’adda.

Malamin ya faɗi haka ne cikin wata sanarwa da aka wallafa a wani shafinsa na Facebook.

Tuni dai ƴan majalisa a Najeriya suka nemi gwamnatin Tarayya ta ayyana ƴan fashin da suka addabi arewacin Najeriya a matsayin ƴan ta’adda.

A cikin sanarwar, Sheikh Gumi ya yi gargaɗin cewa “da zarar an ayyana ƴan fashin daji a matsayin ƴan ta’adda ƙungiyoyi masu da’awar jihadi na ƙasashen waje za su samu gindin zama.

Ya kuma ce wannan zai iya janyo ra’ayin matasan da ke fama da rashin aikin yi.

“Babu wanda ke shakkar cewa son raine a yau ya mamaye siyasarmu. Don ci gaba, dole ne wasu su fito su yi magana,” a cewar Sheikh Gumi.

Sai dai kuma a cikin bayanansa malamain ya ce ayyukan da ƴan fashin daji ke aikatawa sannu a hankali sun na ta’addanci – “saboda duk inda ake kashe mutanen da ba su ji ba su gani ba, ta’addanci ne tsantsarsa.”

Labarai Makamanta