Za A Yi Bikin Karɓar Ahmed Musa A Kano Pillars

Kyaftin ɗin Najeriya Ahmed Musa ya cimma yarjejeniyar komawa tsohuwar ƙungiyarsa ta gida, Kano Pillars inda zai taka mata leda har zuwa ƙarshen kaka.

Daga cikin sharuɗan da aka cimma da shi kafin cimma yarjejeniyar akwai damar iya barin ƙungiyar a duk lokacin da ya samu inda zai koma a Turai.

Ya ce zai bugawa Pillars ɗin ne domin haɓɓaka wasanninsu da martabarsu da kuma taimakawa shi kansa ya ci gaba da zama cikin kuzari, yayinda yake laluben kulob ɗin da zai saye shi a Turai.

Ahmed Musa na ƙoƙarin ganin yada zai ci gaba da zama kan ganiyarsa zuwa wasannin samun gurbi a gasar cin kofin duniya da za a soma a watan Yuni.

Ɗan wasan mai shekara 28, ya bar ƙungiyar Al Nassr ta Saudiyya a watan Oktoba, kuma tun daga wannan lokaci yake samun tayi daga ƙasashen Ingila da Rasha da Turkiyya.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da shugaban league na Najeriya Shehu Dikko ne suka bashi shawarar daukan wannan mataki.

Labarai Makamanta