Za A Wadata ‘Yan Sanda Da Kayan Aiki Domin Fuskantar Zaben 2023 – Shugaban ‘Yan Sanda

Sifeta janar na ƴan sandan Najeriya Usman Alkali ya bayar da umurnin bai wa ƴan sandan ƙasar sabbin kayan sawa da na aiki domin su samu damar gudanar da aikin zaɓen shekara ta 2023 yadda ya kamata.

Baya ga sabbi kayan sarki, sauran kayan da za a bai wa jami’an ƴan sandan sun haɗa da na korar masu zanga-zanga, da rigar surke, da hular kwano, da hayaƙi mai sa hawaye da sauran su.

Sifeta janar na ƴan sandan ya ce waɗannan kaya za su taimaka wa ƴan sandan wajen gudanar da ayyukansu gabanin babban zaɓen ƙasar na 2023, da lokacin zaɓen da kuma bayansa.

Wannan umurni na zuwa ne bayan kayan da aka sayo na ƴan sanda domin inganta walwalar jami’an hukumar, yayin da ake ci gaba da ganin yadda za a tabbatar da ƙwarewa wurin aiki.

Sai dai IGP Usman Alkali ya buƙaci jami’an hukumar da su kare martabar aikinsu da kuma kare hakkin al’umma.

Labarai Makamanta