Za A Samar Da Jami’an Tsaro A Tashoshin Jiragen Kasa – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta samar da jami’an tsaro na musamman da za su riƙa kula da sufurin jiragen ƙasa a wani ɓangare na matakan magance hare-haren da ake kai wa jiragen da fasinjoji a ƙasar.

Ƙaramin ministan sufuri na ƙasar Ademola Adegoroye ne ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyara tashar jirgin ƙasa ta Tom Ikimi a ƙaramar hukumar Igueben da ke jihar Edo, wadda ‘yan bindiga suka kai wa hari a ƙarshen makon da ya gabata tare da yin garkuwa da fasinjoji.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar sufurin ƙasar ya fitar, ya ce gwamnatin ƙasar za ta ɗauki matakan da suka dace domin magance matsalar hare-hare kan tasoshin jiragen ƙasa domin tabbatar da kariya ga fasinjoji da kayayyakin aikin hukumar.

Daga cikin matakan da ya ce hukumar za ta ɗauka har da haɗa kai tsakanin hukumar da al’umma mazauna yankunan da tasoshin jiragen suke domin samar da tsaro da tasoshin jiragen.

Haka kuma ministan ya yi watsi da fargabar da ake yi na cewa gwamnati za ta rufe zirga-zirgar jiragen ƙasa a faɗin ƙasar, yana mai cewa gwamnatin tarayya da hukumar sufurin jiragen ƙasa ba su da wannan niyya, sanna kuma za a ci-gaba da sufurin.

Labarai Makamanta