Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta ce tana shirin rufe sansanonin ‘yan gudun hijira a fadin ƙasar.
Babbar kwamishiniya a ma’akatar kula da ‘yan gudun hijira da kuma ‘yan cirani, Imaan Sulaiman-Ibrahim ce ta bayyana hakan a ranar Juma’a yayin raba wa ‘yan gudun hijra guda 100 kayakin yin sana’o’i a wasu sansanoni da ke Abuja, babban birnin ƙasar.
Ta ce wadanda aka raba wa kayayyakin suna samun horo a fannin sana’o’i daban-daban domin samun kwarewa.
Ta ce hakan na cikin wani shiri da gwamnati ke yi na rufe sansanonin ‘yan gudun hijira a fadin ƙasar domin wadanda rikice-rikice ya ɗaiɗaita su samu damar komawa gidajensu.
Ya zuwa watan Agustan 2022, Najeriya na da sansanonin ‘yan gudun hijira miliyan 3.4, sai dai bayan mummunar ambaliya ta ɗaiɗaita al’ummomi a fadin ƙasar, alkaluman sun ƙaru zuwa miliyan 5.
You must log in to post a comment.