Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Za A Rage Yawan Fursunoni A Gidajen Yari – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta ce tana son ƙara rage yawan fursunonin da ke cikin gidajen gyara hali da ke faɗin ƙasar domin rage cunkoso.

Mai bai wa Ministan harkokin cikin gida shawara kan harkokin watsa labarai Sola Faure ne ya tabbatar wa manema labarai hakan inda ya ce tuni ministan wato Rauf Aregbesola ya aika takarda ga gwamnonin ƙasar domin neman haɗin kansu.

Ministan harkokin cikin gida na Najeriya Rauf Aregbesola ya bayyana cewa yana so ya tattauna da gwamonin ƙasar domin sakin aƙalla kashi talatin cikin ɗari na fursunonin da ke gidajen gyaran hali a fadin ƙasar.

Ya bayyana cewa akwai buƙatar yin hakan sakamakon kashi 90 cikin 100 na fursunonin ƙasar an tsare su ne sakamakon saɓa dokokin jihohi inda ya ce akwai kimanin fursunoni 75,635 da ke zaman jiran shari’a.

Mista Aregbesola ya bayyana cewa jimillar waɗanda suka saba dokokin gwamnatin tarayya da ke tsare a gidajen gyaran hali ba su wuce kashi 10 cikin 100 ba inda ya ce sauran waɗanda ke tsare duk suna da alaƙa ne da saɓa dokokin jihohi.

Exit mobile version