Za A Maka Ministan Lantarki A Kotu

Ministan Makamashi ya sa an yanke Wutan Gidan Makwabcin sa, Dan Takaran Shugabancin Jam’iyyar APC na Kasa a Jalingo.

An zargi Ministan Makamashin wutar Lantarki, Sale Mamman da bada umurni ga Hukumar Wutar Lantarki na Yola, dake Jalingo da su
cire wutan Gidan Makwabcin na sa, Dan Takaran Shugabancin Jamiyyar APC na Kasa, Barista Muhammad Bello Mustapha.

Da misalin karfe hudu da rabi na yammacin Ranar Asabar ne Hukumar Wutan Lantarki na Yola dake Jalingo, ta yanke wutan bisa ummurnin Ministan Makamashi Sale Mamman kamar yanda Muhammad Bello Mustapha yayi zargin.

“Nayi magana da wadanda sukazo yanke wutan Gidana kuma sun shaida min cewa, umurni ne da Ministan Makamashin Wuta, Sale Mamman ya bamu na mu cire wutan ko kuma a koremu a aiki”

Mustapha na ikirarin cewa hakan bai rasa nasaba ne da karban bakoncin da yayi na Dantakaran Gwamnan Jihar Taraba, Chief David Sabo Kente a Gidansa don ta’aziyyar Tsohuwar Ministan Mata, Maman Taraba, bayan fitowanshi daga Fadar Mai Martaba Sarkin Muri, ya fusata Ministan.

“Ni dai dan Kasane, kuma cikakken Dan Jam’iyyar APC mai biyayya da koyi da dabi’ar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, na dade ina aiki da Shugaban Kasa, inda na jagoranci Matasa a Kungiyar (BSO) da sauransu, kuma ina mai koyi da halayenshi, kuma Chief David Sabo Kente (DSK) ma cikakken dan Jam’iyyar APC ne mai neman Takaran Kujeran Gwamnan Taraba a APC, kuma ina mai Addu’ar idan shine mafi Alkhairi a Jihar, Allah Ya bashi nasara. Kuma ai Ministan makwabci nane kuma bai taba gayamin cewa yana neman Gwamna ba” Inji MB Mustapha.

Dan Takaran Shugabancin Jamiyyar APC na Kasa yace matsayin shi na wanda Ya san Doka, kuma dan Kasa da baya fashin biyan kudin wutan gidan sa, zai garzaya Kotu domin bin hakkin sa.

M.B Mustafa ya kuma baiwa magoya bayanshi hakuri da kada su dauki mataki a hannun su, zaiyi dukkanin mai yiyuwa kamar yadda Doka ya tanada wurin kwato hakkinsa da aka tauye .

Aeron Artimas shine Mataimaki na Ministan Makamashin Wutan Lantarki kan harkaokin yada Labarai, inda yace ko kadan Ministan bashida hanu cikin yanke wutan Gidan Bello Mustapha.

“Ban tabajin dai-dai da rana daya Minista yace yana fada da Dan Takaran Neman Gwamnan Taraba, David Sabo Kente ba, ko Barista MB. Mustapha, hasalima tare suka shigo Jirgi zuwa Jalingo a lokacin da suka zo sabunta Rigistar su na Jam’iyya a kwanakin baya “.

Mista Artimas ya kara da cewa “ai shi masanin Shari’a ne, sai ya garzaya Koto, yafi sanin abinda zaiyi ai”.

Muryar Yanci, ta tabbatar da cewa, lokacin da ake yanke wutar, Ministan Makamashi, Sale Mamman na nan a cikin Gidansa dake Jalingo.

Labarai Makamanta