Za A Kori Jami’an SARS 37 Daga Aiki – Hukumar Kula Da ‘Yan Sanda

A kalla jami’an tsohuwar rundunar ‘yan Sanda masu yaki da fashi da makami da sauran muggan laifuka (SARS) guda 37 ne ake shirin sallama daga aiki bayan wani binciken ƙwaƙwaf da aka gudanar a kansu, akan yadda suka mu’amalanci mutane lokacin da suke gudanar da aiki.

Ana kuma tsammanin hukumar kula da ‘yan sanda, PSC, za ta bada umurnin tuhumar wasu jami’an SARS 24 da ake zargi da aikata laifuka da dama da suka saba dokar aikinsu.

Wadannan sune wasu daga cikin manyan abubuwan da ke cikin rahoton da kwamiti da shugaban kasa ya kafa don yi wa rundunar ta SARS garambawul a 2018 ya kunsa.

Kwamitin na Shugaban kasa ya binciki zargin keta hakkin dan adam da amfani da karfin da doka ta bada ba bisa ka’aida ba da ake zargin wasu jami’an na SARS da aikatawa.

Da ya ke mika rahoton ga shugaban PSC, Musliu Smith a Abuja a ranar Juma’a, sakataren hukumar kiyayye hakkin dan adam, Tony Ojukwu ya bukaci a gagauta zartar da shawarwarin da kwamitin ya bayar.

Sanawar da kakakin PSC, Ikechukwu Ani ya fitar ta ce Ojukwu yana kyautata tsammanin cewa shugaban na PSC zai aiwatar da shawarwarin da ke cikin rahoton kwamitin na shugaban kasa. Har wa yau, kwamitin ya bukaci Sufeta Janar na ‘yan sanda ya bayyana sunayen jami’ai 22 da aka samu da laifin keta hakkokin dan adam da cin zarafin mutanen da basu-ji-basu-gani-ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply