Za A Kori Duk Ministan Da Aka Samu Da Rashin Katabus – Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 11 ga watan Oktoba ya karanto dokar da ta shafi bibiyar ayyukan ministoci a majalisar ministocinsa da sakatarorin dindindin a fadin ma’aikatu.

An tattaro cewa shugaban ya bukaci Ministocin da su dauki batutuwan aiwatar da ayyukan da aka dora masu da muhimmanci. Shugaban ya ce yana da mahimmanci Ministocin su sani cewa sauke nauyin ayyukansu da muhimmanci zai taimaka wa gwamnatin yanzu ta cimma burin ta da alkawuran da ta yiwa ‘yan Najeriya.

Shugaban ya fadi haka ne a taron bitar ayyukan ministoci na rabin wa’adinsa na kwanaki biyu da aka shirya don tantance ci gaban da gwamnatin shugaba Buhari ke kawowa.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce Buhari ya yi wannan jawabi ne yayin da ya ke kaddamar da tsarin gudanar da ayyuka na fifiko na shugaban kasa.

Ya ce tsarin ya fara aiki tun daga watan Janairun 2020 kuma ya baiwa gwamnati damar bibiyar ayyuka a zahirance tare da samun bayanan da suka dace kuma ake bukata, da kuma ɗaukar matakan da suka dace ga Ministocin da suka gaza yin wani katabus.

Adesina ya ce shugaban ya kuma yi alkawarin zai zauna domin sauraron jimillar kimar ayyukan majalisar ministocinsa da na ma’aikatunsa cikin shekaru biyu da suka gabata.

“Hakanan, Shugaban zai shiga cikin tattaunawa kan mafi kyawun dabarun aiwatar da tsare-tsare, shirye-shirye da ayyukan da za su iya habaka tattalin arziki sosai daga dogaro da kudaden shiga na mai, tare da ci gaban tattalin arzikin da ake samu a halin yanzu.”

Labarai Makamanta