Za A Kashe Miliyan 999 Wajen Ciyar Da Dalibai – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta riƙa kashe naira miliyan 999 a kullum wajen ciyar ‘yan makarantar firamare miliyan 10 a kowace rana a shirin ta na ciyar da ɗalibai, wato ‘National Home Grown School Feeding Programme’ (NHGSFP) da ta ke gudanarwa a duk faɗin ƙasar nan.

Shugabar gungun ma’aikatan da ke gudanar da shirin, Hajiya Aishatu Digil, ita ce ta bayyana haka a ranar Talata a Abuja a wajen wani taro na masu ruwa da tsaki da aka yi kan hanyoyin rarraba abincin da sake duban fasalin kuɗin da ake kashewa a shirin.

Ta ce Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta samo amincewar a riƙa kashe N100 a kan kowane yaro a kullum a shirin.

Ta ƙara da cewa daga yanzu, za a riƙa kashe N100 a kullum wajen ciyar da kowane daga ‘yan makaranta 9,990,862 ‘yan ajin firamare ɗaya zuwa aji uku da ke cikin shirin da a kullum a tsawon kwana 20 a wata, wanda jimillar kuɗin ya kama N999,086,200 a kullum.

Ta ce, “A da kafin yanzu, mu na kashe N70 ne wajen ciyar da kowane yaro, a abinci zaman ci ɗaya. Haka mu ke yi tun daga 2016, amma yanzu shugaban ƙasa ya amince a ƙara kuɗin zuwa N100.

“Mu na da masu ruwa da tsaki irin su Shirin Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (World Food Programme), da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (National Bureau of Statistics), da Hukumar Faɗakarwa ta Ƙasa (National Orientation Agency, NOA), da Ƙungiyar Inganta Abinci ta Duniya (Global Alliance for Improved Nutrition, GAIN), da Ma’aikatar Aikin Gona da ta Ilimi, da ma wasu, da za su tattauna kan hanyoyin rarrabawar.

“Mun taru a nan ne domin mu kalli hanyar da ta fi dacewa mu yi amfani da ita wajen samun alfanun shirin bisa sabon tsarin kashe kuɗi don inganta kyawun abinci da ake ba yaran.

“Lissafin kashe N100 ɗin shi ne: N70 shi ne kuɗin dukkan kayan haɗa abincin amma ban da ƙwai, sai N14 kuɗin ƙwai da za a riƙa saye ta hanyar gwamnatocin jihohi da haɗin gwiwar Ƙungiyar Makiyaya Kaji ta Nijeriya (Poultry Association of Nigeria).

“Mu na tsara fitar da ranar da za mu kira ‘Larabar Cin Ƙwai’ (‘Egg Wednesday’), inda za a riƙa ba kowane yaro da ke cikin shirin ƙwai guda ɗaya a kowace ranar Laraba; sai N10 ta ladar masu girki, N5 da N6 na tabbatar da lafiyar abinci wanda za a riƙa ba masu girkin, da kuma naira ɗaya ta tabbatar da inganci, wadda za a ba jami’ai masu sa ido, wanda wannan zaɓi ne.”

Digil ta ce shirin zai tabbatar da an tsame muggan halayen aiwatarwa, ta ƙara da cewa ma’aikatar na so ta kawo gyare-gyare.

Ta ce, “Bayan wannan taron, za mu tattaro shawarwarin masu ruwa da tsaki, sannan mu miƙa su ga minista saboda mu aiwatar da sabon tsarin kuɗin ciyarwar, wanda zai fara daga wannan watan.”

Labarai Makamanta