Za A Kashe Biliyan 396 Wajen Sayen Rigakafin Korona – Ministar Kuɗi

Gwamnatin Tarayya tana tsara kashe Naira biliyan 396 don yin allurar rigakafin Korona a shekarar 2021 da 2022, domin shawo kan matsalar cutar wadda ke addabar Duniya gaba ɗaya.

Ministar Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Kasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a ranar Laraba bayan taron mako-mako na Majalisar Zartarwa ta Tarayya, wanda Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Zainab ta bayyana cewa wannan adadi na iya raguwa matuka kasancewar Gwamnatin Tarayya na karbar karin gudummawar allurar rigakafin daga kamfanoni masu zaman kansu.

Ministar Kuɗin ta ƙara da cewa Ma’aikatar Lafiya na aiki kan cikakkun bayanai game da gibin da za a bukaci Gwamnatin Tarayya ta cika a aikin yin allurar rigakafin.

Ta kuma bayyana cewa girman kasafin kudin da aka gabatar wanda bangaren zartarwa da bangaren majalisa suka amince dashi har yanzu ba a warware shi ba, saboda Ma’aikatar Tsaro da Lafiya, har yanzu ba ta ba da cikakken bayani game da kayan aikin sojan ba.

Labarai Makamanta