Za A Kara Farashin Kudin Kiran Waya A Najeriya

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar da ke kula da harkokin sadarwa ta ƙasa ta ce ta samu takarda daga ƙungiyar kamfanonin sadarwa na ƙasar na neman yin ƙarin kuɗin kiran waya da kuma data sakamakon tsadar gudanar da ayyukansu.

Rahotanni sun ce takardar da ƙungiyar ta gabatar na neman yin ƙarin kashi 40 cikin 100 na farashin kiran waya da aika saƙo.

Kamfanonin na son yin ƙarin ne na kira daga N6.4 zuwa N8.95, farashin aika saƙo kuma zai koma N5.61 maimakon N4.

Hauhawan farashi a Najeriya kusan ya shafi ko wane ɓangare, yayin da masu saye da sayarwa suka fi jin tasirinsa.

Taɓarɓarewar darajar naira ya ƙara haifar da tsadar kayayyakin, musamman a ƙasar da ta dogara da shigo da kayayyakin buƙatu na yau da kullum daga waje.

Labarai Makamanta