Za A Kara Daukar Matasa Dubu 400 Aikin N-Power – Ministar Jin Kai


Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministar Ayyukan Agaji, Jinƙai da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq ta bayyana cewa kwanan nan za a ƙara ɗaukar matasan N-Power 400,000.

Ta yi wannan albishir ne ranar Laraba a Kano, lokacin da ta ke jawabi wurin rufe kwas ɗin horas da matasa fasahar N-Knowledge a Kano, waɗanda aka kammala horar da su a ƙarƙashin Rukunin C.

Minista Sadiya ta ce ƙarin matasa 400,000 ɗin da za a ɗauka duk su na cikin matasa miliyan ɗaya da Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a samar wa tudun-dafawa a ƙarƙashin shirin N-Power.

“Shirin Kashi na C1 ya ƙunshi matasa 510,000, sai Kashi na C2 da za a ɗauka kwanan nan, su kuma 400,000 ne.” Inji Minista.

Sadiya ta ce, “Tsarin N-Knowledge shiri ne da aka ƙirƙiro shi domin horar da matasa 20,000 fasahar ayyukan kwamfuta masu tafiya da zamani, tare da ba su takardun shaidar ƙwarewa a fannonin da su ka samu horo a kai, ta yadda za su iya samun ayyukan dabarun fasahar zamani a cikin ƙasar nan da sauran ƙasashen duniya.

“Kuma za su samu ƙwarewa sosai wajen dabaru da fasahar ƙirƙirar ababen samar da ci gaba da kuma dabarun sana’o’in hannu a zamanance a cikin ƙasa ko sauran ƙasashen duniya.”

Daraktan Harkokin Kuɗaɗe Muhammad Sambo ne ya wakilci Minista a bikin yaye matasan su 3,000 da aka yi ranar Laraba a Kano, waɗanda aka zaɓo daga cikin dukkan jihohin Arewa maso Yamma.

Ya ce a yanzu an horas da matasa 13, 000 a faɗin ƙasar nan. Kuma ana nan za a zaƙulo cikon ragowar 7,000 daga ko’ina cikin ƙasar nan.

Labarai Makamanta