Za A Kara Albashin Ma’aikata A Shekarar Badi – Gwamnatin Tarayya

Ministan ƙwadagon Nijeriya Chris Ngige ne ya sheda hakan ga manema Labarai

Ya fara da cewa nan ba da jimawa ba gwamnatin tarayya za ta bayyana ƙarin albashi ga ma’aikatan gwamnati a ƙasar domin rage raɗadin tashin farashin kayyaki da ake fuskanta a ƙasar a halin yanzu.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan ya yi wata ganawar sirri da shugaban ƙasar Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Aso Villa A Birnin tarayya Abuja.

Ya ce kwamiti kan albashi da shugaban ƙasar ya kafa na sake duba batun albashin ma’aikata a ƙasar, kuma ana sa ran zai zo da buƙatar ƙarin albashin a shekara mai kamawa ga Daukacin Maaikatan kasar lura da hauhawan farashi da ake fuskanta ga kuma Albashi na Tsaye gu guda.

Da aka tambaye shi ko sun tattauna wannan batu tare da shugaba Buhari, sai ministan ya ce ”ƙwarai kuwa, wannan shi ne abin da nake faɗa cewa kwamitin albashi da shugaban ƙasar ya kafa na aiki kafaɗa-da-kafaɗa da hukumar albashin ma’aikata ta ƙasar”.

“Dan haka yayin da muka shiga sabuwar shekara gwamnatin tarayya za ta ayyana batun ƙarin albashin”, in ji ministan.

Labarai Makamanta