Za A Kammala Titin Abuja Zuwa Kano A 2023 – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin kammala aikin hanyar Aabuja zuwa Kano zuwa Kaduna a shekarar 2023.

Karamin Ministan ayyuka da gidaje Abubakar D. Aliyu ya bayyana haka a ranar Alhamis, lokacin da ya jagoranci tawagar ma’aikatarsa zuwa wata ziyara a Kano.

A cewar Ministan, an raba aikin ne gida uku, da wanda ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna, Kaduna zuwa Zaria sai kuma Zaria zuwa Kano, domin tabbatar da an hanzarta kammala aikin.

A kan korafin da ake na rashin saurin aikin, ministan ya alkanta hakan ga yadda kamfanonin da ke aikin ke gogayya da matafiya a hanya guda, wanda hakan ke zama kalubale garesu.

Daga nan ya yi kira ga jama’a da su kara hakuri yana mai cewa gwamnatin tarayya na yin dukkan mai yiwuwa don ganin an gama aikin ba tare da an kara samun tsawaita lokaci ba.

A cikin watan Yunin shekarar 2018 ne dai aka fara aikin hanyar tare da alkawarin kammalawa cikin wata 36.

Labarai Makamanta