Za A Halastawa Mace Auren Namiji Fiye Da 1 Lokaci Guda A Afirka Ta Kudu

Ma’aikatar harkokin cikin gida na kasar Afrika ta kudu ta sanar da cewa tana shirin kafa sabuwar dokar halastawa mata auren namiji fiye da daya kamar yadda maza ke auren mace fiye da daya.

A cewar rahoton iharare, sabuwar dokar za tayi bayani game da salon auratayyan da basu hallata ba. Rahoton yace takardar da ma’aikatar ta fitar wannan makon ya nuna cewa babu adalci da daidaito kan dokar auren da ake amfani da shi yanzu.

Daga cikin rashin adalcin shine dokar bata hararo salon auren mabiya addinin Hindie, Yahudu, Musulmi da Rastafarian ba. Takardar ta bukaci a sanya sabon salon aure inda mace za ta samu yancin auren namiji fiye da daya.

Sarakunan gargajiya a kasar Afrika ta kudu sun nuna rashin amincewarsu da wannan shiri da akeyi inda suka bayyana cewa “wannan abu ya sabawa al’adar al’ummar Afrika.”

Amma ma’aikatar ta mayar da martanin cewa: “Abin takaici shine wadanda suka yarda namiji ya auri mace fiye da daya ne suke adawa da mace ta auri namiji fiye da daya.”

Rahotanni sun bayyana cewa an baiwa yan kasar zuwa karshen watan Yuni su tofa albarkatun bakinsu kafin a yanke shawara kan lamarin.

Labarai Makamanta