Za A Gudanar Da Babban Taron APC A Fabrairun Badi

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyyar APC mai mulki ta ce za ta gudanar da babban taronta na kasa a watan Fabrairun shekarar 2022.

Shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar ta APC kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu ne ya bayyana haka ga manema labaran da ke fadar shugaban kasa ranar Litinin bayan ganawa da Muhammadu Buhari.

Shugaban kungiyar gwamnonin na APC ya gana da shugaban kasar ne tare da rakiyar shugaban riko na jam’iyyar kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Malla Buni da kuma gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru.

Gwamna Bagudu ya ce sun zabi gudanar da taron a watan Fabrairu ne domin bayar da dama ga jihohi hudu su kammala zabukansu na cikin gida sannan kuma ‘yan kasar su samu damar kammala bukukuwan Kirsimieti da na sabuwar shekara.

A yayin da yake jawabi, Gwamna Buni ya ce ba su tsayar da ranar gudanar da taron ba ne saboda su samu damar sanar da hukumar zabe mai zaman kanta da kuma duk wasu masu ruwa da tsaki.

Labarai Makamanta