Za A Gudanar Da Aikin Hajjin Bana – Saudiyya

Gidan talabijin na Saudiyya ya sanar da cewa za a kyale maniyyata su gudanar da aikin hajjin bana amma karkashin wasu sharuda.

“Yadda za a yi da kuma sharudan yin za a sanar da su daga baya” in ji ma’aikatar aikin Hajji ta Saudiyya.

A shekarar da ta gabata Saudiyya ta bar wasu tsirarun mutane gudanar da aikin Hajjin kuma wadanda kawai suke zaune a kasar, ba a bar kowa daga waje ya yi ba.

Sauyin da aka samu dai na da alaka da wannan annoba ta korona wadda ta damu duniya baki daya.

Labarai Makamanta