Za A Gina Masana’ata A Kowace Mazaba A Najeriya – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta kafa akalla masana’anta daya a kowacce mazaba cikin mazabun yankin majalisar dattawa 109 a fadin tarayya.

Karamar Ministar ma’aikatar masana’antu, kasuwanci , da zuba hannun jari, Ambasada Mariam Yalwaji Katagum, ta bayyana haka ne ranar Alhamis a Jihar Kano a yayin da ta kai ziyarar ban girma ga gwamna Abdullahi Ganduje.

Ministar ta ziyarci jihar ne domin kaddamar da cibiyar kanikanci na zamani da ofishoshi a masana’antar koyar da aikin hannu. `A jawabinta, ta alanta shirin kafa masana’antu sarrafa kayan noma a sassan Najeriya shida, kuma an fara tattauna lamarin a zaman mako-mako na majalisar zartarwar tarayya.

Tace ”Ya nada muhimmanci in fara janyo hankalin mutane kan cewa nan da shekara mai zuwa, za’a kaddamar da wadannan masana’antun sarrafa kayayyakin gonan kuma dukkan sassan kasa zasu samu nan da 2023”.

A nasa jawabin, Gwamnan jihar kano, Abdulahi Ganduje ya bayyana cewa Kano gari ne na kasuwanci da masana’antu, kuma za’a kara samar da masana’antu a Jihar.

Related posts