Za A Garƙame Duk Wanda Aka Kama Yana Tashe A Katsina

Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar Gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari tae haramta al’adar Tashe da ake yi cikin watan Ramadana, a dukkanin faɗin jihar

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da al’adu da harkokin cikin gida Abdulkarim Yahaya Sirikathe ya fitar, an dauki matakin saboda dalilai na tsaro kwana 15 da fara azumin.

Gwamnatin jihar ta kuma umarci jami’an tsaro su kama duk wanda aka samu ya ketare dokar.

Gidan Talbijin na Channels ya rawaito kwamishinan na kira ga jama’a musamman iyaye su sa ido kan yayansu su kuma hana su yin tashen a sassan jihar.

Labarai Makamanta