Za A Fuskanci Matsananciyar Yunwa A Najeriya – Majalisar Dinkin Duniya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta tabbatar da cewa ‘yan Najeriya miliyan 19.4 ne za su yi fama da yunwa da barazanar rashin abinci a watannin Yuni zuwa Agustan bana.

Hukumar ta yi wannan bincike tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Harkokin Gona ta Tarayya da wasu Cibiyoyi masu ruwa da tsaki a harkar noma.

Rahoton ya yi nazarin matsalar ƙarancin abincin da za a fuskanta da kuma rashin abinci mai gina jiki a yankunan Sahel da Afrika ta Yamma.

Rahoton ya ƙara da cewa matsalar abinci za ta fuskanci jihohi 21 a Najeriya tare da yankin birnin tarayya Abuja.

An kuma yi kirdadon ‘yan gudun hijira 416,000 ne za su tsinci kan su cikin wannan mawuyacin halin tasku.

Sannan kuma rahoton ya nuna a yanzu haka mutum miliyan 14.4 da kuma masu gudun hijira 385,000 sun afka cikin wannan halin fitinar ta ƙarancin abinci.

Jihohin da aka yi nazari sun haɗa da Abiya, Adamawa, Benuwai, Barno, Cross Riba, Edo, Enugu, Gombe, Kaduna, Jigawa, Kano, Katsina, Kebbi, Legas, Neja, Filato, Sokoto, Taraba, Yobe da Zamfara, da Abuja.

Labarai Makamanta

Leave a Reply