Za A Fuskanci Matsananciyar Yunwa A Najeriya – Bincike

Rahoton dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wani bincike ya nuna cewa za a fuskanci tsananin tsadar abinci a Najeriya wanda hakan zai sabbaba yunwa saboda karancin noma a yankunan kasar.

Hakan na zuwa a daidai lokacin da hukumar kididdiga ta Najeriya NBS ta sanar a rahotonta na watan Satumba cewa farashin shinkafa da kwai da garri da kuma tumatur ya tashi sosai.

Yanzu haka a Najeriya ana kokawa kan tsadar buhun shinkafa da ya tasarma kusan naira 30,000.

Hakama rahoton na NBS ya ce farashin kwai ya karu a wasu wuraren da kusan kashi 25 cikin 100.

Kazalika a wasu kasuwannin ana sayar da kilon tumatur akan naira 342, a maimakon naira 286 a watan Satumba.

A daya waje NBS ta bayyana cewa an samu tsadar sufuri a mota da jiragen sama da na kasa da ke fadin Najeriyar.

Haka kuma wani bincike da kamfanin United Capital Management ya yi, ya gano cewa hauhawar farashin kayan abinci da aka samu daga watan Satumba zuwa yanzu, manuniya ce ga irin halin tsadar farashin kayan abinci da kasar za ta iya shiga badi.

Labarai Makamanta