Za A Farfado Da Sufurin Motocin Haya A Abuja – Hukumar Birnin Tarayya

Rahoton dake shigo mana daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a yayin da harkoki ke ci gaba da bunkasa da mutane, wata matsala da ake fuskanta a birnin ita ce ta sufuri musamman na motocin haya.

Sufuri a birnin dai na da matukar muhimmanci saboda yawan ma’aikatan da ake da su kama daga na gwamnati da ma na kamfanonin masu zaman kansu, wannan ne ya sa sufuri ke da muhimmancin gaske a Abuja.

Bisa la’akari da muhimmancin na sa ne hukumar babban birnin tarayyar, ta karfafa wa kamfaninta na harkokin kasuwanci da masana’antu da sauransu, wato Abuja Investment Company Limited, gwiwa a kan ya farfado da kamfaninsa na motocin sufuri, ta yadda zai rika gudanar da harkokin sufuri a yankin babban birnin tarayyar yadda kamata, kuma da inganci.

Abubakar Maina Sadiq, shi ne babban jami’in kamfanin harkokin kasuwanci da masana’antun na Abuja, ya shaida wa BBC cewa bisa la’akari da muhimmancin sufuri a birnin, ya sa aka fara tunanin farfado da kamfanin sufurin.

Labarai Makamanta