Rahotanni daga Dutse babban birnin Jihar Jigawa na bayyana cewa Gwamnatin Jihar ta bayyana cewa komai ya kankama don fara biyan mata masu juna biyu sama da 5000 kudi dubu biyar-biyar a duk wata.
Mataimakain Gwamnan Jihar, Mallam Umar Namadi, ya bayyana haka a yayin wata ganawa da manema labarai a Dutse, babban birnin Jihar.
Namadi yace jihar ta bullo da shirin ne domin ya taimaka wa mazauna karkara don su rika zuwa awon ciki a asibiti kafin haihuwa.
Ya ce gwamnatin Muhammad Badaru ta sanya wannan kudi cikin kasafin kudin 2022 da Gwamnan ya sanya wa hannu. Ya kara da cewa an bude wa kimanin mata 3,800 asusun ajiya na banki kuma za a fara biyansu a watan Fabrairun 2022,
You must log in to post a comment.