Za A Fahimci Rawar Da Muka Taka Bayan Mun Bar Mulki – Shugaban Majalisa

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya bayyana cewa mafi yawan ‘yan Najeriya na kwana da tashi cikin farin ciki da ‘yan majalisa. Wannan farin cikin kuwa, jin daɗi ne da su ke yi ga mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.

Lawan ya ce sai ma bayan sun kammala wa’adin mulkin su ne akasarin ‘yan Najeriya za su riƙa santin rubutawa da furta kalaman alheri kan Majalisar Dattawa da ta Tarayya, dangane da ɗimbin nasarorin da suka samar.

Lawan ya yi wannan bayani ne a wurin wani taron taya shi murnar cika shekaru 63 a duniya, wanda aka shirya a ranar Laraba, a Abuja.

Labarai Makamanta