Za A Aurar Da Karuwai A Bauchi

Gwamnatin Bauchi ta ce za ta mayar da kowacce mace mai zaman kanta jiharta ta asali.

Sannan cikin matan wadanda suka kasance ƴan asalin Bauchi za a sama musu maza a aurar da su, Hisbah za ta taimaka wajen shirya auren da sayayen kayan daki da hidimar biki

An rawaito cewa kwamishinan da ke kula da hukumar Hisbah ta jihar, Barr Aminu Balarabe Isah ne ya shaida haka a wani taron wayar da kai gabanni soma azumin Ramadan wanda aka gudanar a yankin Bayan Gari da ke tsakiyar birnin Jihar.

A cewar jaridar, ya kuma shaida yadda hakan zai ba su damar komawa suyi rayuwa mai mutunci.

Ya ce bincikensu ya gano cewa yawanci mata na faɗawa cikin irin wannan munanan aiki ne bisa tsangawama ko talauci ko cin zarafi da rashin ilimi.

Wasu kuma a cewarsa kishiyoyi ke jafa su cikin karuwanci.

Barr Isah, ya ce a yanzu za suyi aiki da sauran gwamnatin jihohi da kananan hukumomi wajen kawo karshen karuwanci da munana dabi’u kuma a samawa matan sana’o’in dogaro da kai.

Labarai Makamanta