Zaɓen 2023: Ba Zamu Yarda Da Murɗiya A Kano Ba – Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya gargadi jam’iyyar APC a jihar cewa PDP ba zata sake amincewa a maimaita mata murdiya ‘inconclusive’ ba kamar yadda aka yi a zaben shekarar 2019 ba.

Sanata Kwankwaso ya ce shi da jam’iyyarsa ta PDP da magoya bayansa ‘yan Kwakwasiyya, ba za su amince a sake maimaita hakan ba sai dai dukkannin abin da zai faru ya faru.

PDP na kan gaba a zaben gwamna a Kano kafin hukumar zabe, INEC, ta ce zaben bai kammalu ba. Daga bisani aka yi zaben raba gardama a wasu yankuna kuma APC ta yi nasara, hakan ya bawa gwamna Abdulllahi Ganduje nasarar zarcewa kan mulki.

Kwankwaso ya yi wannan jawabin ne a ranar Alhamis, yayin da ya ke yi wa magoya bayansa jawabi inda suka rika jinjina masa. Daga bisani an wallafa bidiyon jawabin a shafin Facebook na Kwankwasiyya da aka saba wallafa labaran siyasa masu alaka da jigon na PDP.

A cikin bidiyon, da Kwankwaso ya yi magana da harshen Hausa, ya ce: “Yanzu sun bugu da giyar mulki ba su tunanin sauka daga mulki domin suna tunanin 2023 ba zata zo ba.

“A tunaninsu, dukkan zunuban da suka aikata, za su hada baki da hukumar INEC da jami’an tsaro a 2023 da wasu shugabanni su maimaita zaben inconclusive da suka yi a Kano a 2019 kuma mu kyalle su?.

“2023 zai banbanta da baya, sai da a mutu ko a yi rai, za mu shirya musu. “A 2023, ina kira ga mata su dauko tabarya da ludayin miya su rike kusa da su (don kare kuri’ansu),” inji Kwankwaso.

Labarai Makamanta

Leave a Reply