Zaɓen 2023: Saraki Ya Roki ‘Yan Najeriya Su Zabi PDP

Tsohon shugaban majalisar dattawar Nijeriya, Dr Bukola Saraki ya roki ‘yan Nigeria su mara wa jam’iyyar PDP baya domin ta samu mulkin kasar a babban zaben shekarar 2023 dake tafe.

Saraki ya yi wannan rokon ne yayin da ya ke kaddamar da wasu ayyuka da shirye-shirye da gwamnan Ifeanyi Okowa na jihar Delta ya aiwatar a jiharsa inda ya ce har yanzu akwai sauran mutane masu nagarta a PDP.

Ya ce a halin yanzu Nijeriya tana cikin mawuyacin hali da suka hada da rashin tsaro da kallubalen tattalin arziki don haka ya bukaci jama’a su sake bawa jam’iyyar PDP wata damar domin su sauya lamuran.

“Na yi farin cikin kasancewa a wannan wurin domin kaddamar da wannan aikin. Shekaru hudu mun zauna tare a majalisa mun kuma yi aiki tare da kai a lokacin da muka yi dokar Lafiya ta Kasa; Na gamsu da irin ayyukan da ka ke yi a Delta.

“Kasar mu na fama da wasu kallubale a yanzu kuma ina kira ga yan Nijeriya su sake ba jami’iyar PDP wata damar domin su ga banbanci. “Yadda gwamnatinka ta mayar da hankali wurin gina jiha da kawo cigaba a Asaba, babban birnin jihar abin yabawa ne da jinjina,” a cewar Saraki.

Labarai Makamanta