Zaɓen 2023: Ina Goyon Bayan Mulki Ya Koma Kudu – Kudu


Mai girma Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya nemi a mayar da mulkin kasa zuwa kudancin Nijeriya a babban zaɓe mai zuwa a shekarar 2023 domin samun nasarar mulkin dimukuraɗiyya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin jawabin da ya yi wurin taron tsaro da habbaka tattalin arziki wurin kaddamar da littafin da tsohon shugaban NIMASA, Dakuku Peterside ya wallafa mai taken “Strategic Turnaround”.

Gwamna Zulum ya kuma yi kira ga jam’iyyar APC mai mulki ta karbi shawararsa ta amince da yarjejeniyar da aka yi a baya na cewa mulki zai koma kudu a 2023.

Gwamnan ya yi amfani da damar wurin danganta rashawa da gwamnatocin baya suka yi da Boko Haram. Ya kara da cewa kuskuren da Nijeriya ta yi ne ya janyo aka samu yan bindiga da ke adabar kasar.

Ya yi ikirarin cewa “Idan Nijeriya ta yi koyi da wasu kasashen Afirka ta tallafawa kasashen da ke makwabtaka da ita, to da tuni da an magance matsalar.”

A cewar gwamnan, karfin soja da sauya tsarin mulkin kasa ba za su magance matsalar ba, yana kira a samar da shugabanci na gari da sauya tunanin mutane.

Labarai Makamanta