Zaɓen 2023: Gwamnonin Arewa Biyar Na Goyon Bayan Mulki Ya Koma Kudu

A daidai lokacin da babban zaɓe na shekarar 2023 ke ƙara ƙaratowa da cece-kucen da ake yi akan inda mulkin ya kamata ya koma tsakanin Arewa da kudu, wasu gwamnonin Arewa biyar sun bayyana cewa wajibi ne mulki ya koma kudancin Najeriya a 2023.

Gwamnonin Sun hada da: 1. Babagana Zulum (Borno) A bikin murnar ranar haihuwan tsohon dan takaran gwamnan Rivers, Dakuku Peterside, Zulum yace: “Tsarin kama-kama alkawari ne mukayi, saboda hakan akwai bukatar mulki ya koma kudu.”

2. Nasir El-Rufai Gwamnan jihar Kaduna, ya ce mulki ya koma kudu a 2023. Yace: “Daga Kudu ya kamata shugaban kasa ya fito a 2023; ban goyon bayan dan Arewa ya zama shugaba bayan Shugaba Muhammadu Buhari saboda yarjejeniyar siyasar Najeriya.”

3. Hakazalika, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce duk da cewa kundin tsarin mulki bai tanadi tsarin karɓa-karɓa ba, akwai bukatar a yi amfani da shi don samun nasara a zaben dake tafe.

4.Gwamna Aminu Masari na Kastina ya yi kira ga karɓa-karɓa a 2023. A cewarsa, don adalci da nuna daidaito, ya kamata a ba kudu damar mulkan Najeriya a 2023.

5. Kwanakin baya, gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya nuna goyon bayansa ga tsarin kama-kama. Ya ce akwai bukatar shugaban kasa yazo daga kudu.

Labarai Makamanta