Zaɓaɓɓen Shugaban Nijar Ya Kawo Ziyarar Farko Najeriya

Shugaban kasar jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya samu kyakyawar tarba daga shugaba Buhari da wasu manyan jami’an sa da suka hada da ministan Abuja Muhammad Bello da kuma gwamnonin Jihohin Sokoto da Zamfara da Yobe da Kebbi da Borno.

Bayanan dake zuwa daga fadar shugaban Najeriya dake Abuja tace shugabannin biyu na ganawar sirri yanzu haka, yayin da ake saran shugaba Buhari da bakon nasa suyi buda baki da yammacin yau.

Bazoum Mohammed ya gaji tsohon shugaban kasa Mahamadou Isssofou a matsayin shugaban Jamhuriyar Nijar sakamakon nasarar da ya samu a zaben da aka yi a Nijar.

Labarai Makamanta