Yunƙurin Kisa: Za A Binciki AbdulJabbar Kabara

Wata Kotun Majistare dake birnin Kano a ranar Juma’a ta umarci kwamishanan ‘yan sandan jihar ya gudanar da bincike kan zargin barazana da yunkurin kisa da ake wa Sheikh Abduljabbar Kabara.

Babban Alkalin Kotun, mai Shari’a Mustapha Sa’ad-Datti, ya bada wannan umurni ne bayan sauraron ƙara da Abdulrahman Nasir, lauyan Sheikh Abdallah Pakistan ya shigar a gaban Kotun.

Umurnin mai lamba KA/CMC14/003/2021, ya bukaci kwamishanan ‘yan sandan ya gabatar da sakamakon bincike gaban kotu daga yanzu zuwa ranar 27 ga watan Maris.

Idan jama’a za su iya tunawa cewa ranar 3 ga Watan Fabarairu, gwamnatin jihar Kano ta dakatar da Sheikh Abduljabbar daga wa’azi kuma ta kulle Masallacinsa.

Bayan haka gwamnatin jihar a ranar 7 ga Fabrairu ta sanar da cewa za ta shirya mukabala tsakanin Kabara da sauran Malaman Kano cikin makwanni biyu.

Bayan makwannin biyu gwamnatin ta shirya mukabala ranar Lahadi, 7 ga Maris 2021. Amma ana sauran ‘yan kwanaki, kungiyar Jama’atu a jawabin da ta saki ta tace babu bukatar mukabala da AbdulJabbar, saboda haka ba ta goyon bayan zaman.

Ana jajibirin mukabalar, kotun majistare ta dakatar da mukabalar sakamakon ƙarar da wani Lauya mai zaman kanshi ya shigar gaban Kotun yana ƙalubalantar zama da Abdul-Jabbar

Labarai Makamanta