Rahotanni daga Jihar Yobe na bayyana cewar Gwamnatin jihar ta bayyana cewa za ta cire Kashi 10% daga albashin ma’aikata a karshen watan Nuwamba domin farfado da fannin ilimin jihar.
Kwamishinan aiyukan cikin gida, yada labarai da al’adun gargajiya na jihar Muhammad Lamin ya sanar da haka wa manema labarai a garin Damaturu ranar Litini.
Lamin ya ce gwamnati ta dauki wannan mataki ne domin a hadu duk gaba daya da ma’aikata da jama’a don gina fannin ilimi mai nagarta a jihar.
Ya ce aiyukkan Boko Haram ya yi wa rayuwar mutane mummunar lahani musamman fannin ilimi.
A ranar 9 ga Nuwamba gwamnan jihar Mai Mala Buni ya kafa kwamitin mutum 21 domin kula da asusun da ya bude don tara kudaden farfado da fannin ilimi a jihar.
“Gwamnati na kira ga mutanen jihar da su hada hannu da gwamnati domin farfado da fannin ilimin jihar.
Idan ba a manta ba gwamnati ta saka dokar ta baci a fannin ilimin jihar.
You must log in to post a comment.