Yobe: Mai Mala Ya Bada Umarnin Rufe Makarantu

Gwamnatin Jihar Yobe ƙarƙashin jagorancin Gwamnan jihar Mai Mala Buni ta ba da umarnin rufe dukkan makarantun kwana a fadin kananan hukumomi 17 na jihar nan take ba tare da ɓata lokaci ba.

Duk da cewa jami’an jihar basu bayyana dalilin rufe makarantun ba, amma an fahimci cewa umurnin ba zai rasa nasaba da sace dalibai ba a jihohin Zamfara da Neja.

Wata majiya a daya daga cikin makarantun ta bayyana cewa umarnin rufe makarantun ya isa gare su da safiyar ranar Lahadi kamar yadda majiyarmu ta Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa, iyaye tare da taimakon jami’an tsaro sun zo da sassafe inda suka kwashe daliban Kwalejin ‘Yan Matan Gwamnati da ke Damaturu. Amma, ya ce umarnin ba zai shafi daliban SSS 3 ba.

Kwamishinan ilimin firamare da sakandare na jihar Dr Sani Idriss, bai samu damar yin tsokaci ba a lokacin da aka shigar da wannan rahoton saboda bai amsa kira ba balle ya amsa sakon tes da aka tura masa.

Jihohin Neja, Zamfara da Kano wasu jihohin ne da suka rufe makarantu kwanan nan, tun bayan jerin hare-hare da ‘yan Bindiga suka kai a jihohin tare da yin awon gaba da tulin ɗalibai Mata.

Labarai Makamanta