Yobe: Kotu Ta Sa Ranar Raba Gardama Tsakanin Lawan Da Machina

Babbar Kotun tarayya da ke zama a Damaturu, babban birnin jihar Yobe ta zaɓi ranar 28 ga watan Satumba, 2022 domin raba gardama tsakanin Bashir Machina da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan akan kujerar Sanata ta Yobe ta tsakiya.

An  ruwaito cewa Machina ya garzaya Kotun Damaturu ne domin neman ta tilasta wa hukumar zaɓe INEC ta buga sunansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na takarar Sanatan Yobe ta arewa a inuwar APC.

Machina ya roki Kotun ta yi dokar da zata tilasta wa INEC karban sunansa a matsayin ɗan takarar APC bayan lashe zaben fidda gwani wanda ya gudana ranar 28 ga watan Mayu. Haka zalika, ya nemi Kotun ta umarci jam’iyyarsa APC ta tura sunansa ga hukumar zabe mai zaman kanta kasancewar shi ya yi nasara a zaɓe.

A ranar 12 ga watan Satumba, Alkalin dake jagorantar shari’ar, Mai Shari’a Fadima Aminu, ta ɗage yanke hukunci bayan lauyoyin kowane ɓangare sun gama gabatar da shaidunsu ga Kotu. Mai Shari’ar ta bayyana cewa za’a sanar da ranar yanke hukunci a lokacin da ya dace ga kowane ɓangare.

Hussaini Mohammed Isa, kakakin Mista Machina, ya amsa da cewa, “Eh ranar 28 ga watan Satumba, 2022 ce ranar yanke hukunci.”

Labarai Makamanta