Yawaitar ‘Ya’yan Gaba Da Fatiha Na Barazana A Kasar Iran – Rahoto

Rahoton BBC Hausa

“Dole ne na zubar da cikin jaririn nan. Wannan wani mataki ne mai tsauri a rayuwata,” a cewar Mitra, ƴar shekara 27 mai aikin ƙawata gidaje da ke zaune a Tehran da abokin zamanta.

Mitra da Mohsen, likita mai shekaru 32, sun tare a gida ɗaya ƙarƙashin wani tsarin aure – tsarin da mace da namiji za su amince su sadu da juna inda kuma yin jima’i kafin aure haramun ne ƙarƙashin dokokin musulunci na Iran.

“Mohsen da ni mun fahimci ƙalubalen da ke gabanmu amma ba mu da wani tanadi na haihuwa a lokacin,” a cewarta.

Yanzu kuma sun sauya ra’ayi inda suke neman samun takardar shaidar haihuwa ga jaririn da za su haifa. Amma duk da ƙoƙarin da suka yi, dole ce ta tursasa masu tunanin zubar da cikin.

Ayar dokar Iran ta 1167 ta bayyana cewa “jaririn da aka haifa ta hanyar zina ba zai kasance huruminsu ba,” wanda hakan ke nufin iyayen da ba su da aure ba su da haƙƙin rikonsa a matsayin ma’aurata kuma mahaifiyar ce kawai za ta iya neman buƙatar a saka sunanta ita kaɗai a takardar haihuwar jaririn.

Ga jaririn kuma, hukumomi sukan adana bayanansa da yadda aka haife shi – wasu bayanai da za su hana su samun wasu ayyuka a gaba.

Duk da cewa babu adadi na hukuma kan irin wannan tsarin tarayyar, amma ya zama gama-gari.

Kuma, bayan gaza magance tsarin, hukumomi na fuskantar ƙalubale na magance matsalar da kuma abin da za a yi da yaran da aka haifa ta hanyar nau’in irin wannan tarayyar.

“Daga ƙarshe, waɗannan yaran dole su karɓi takardun haihuwarsu domin samun damar shiga makaranta,” kamar yadda mataimakin ministan kula da harakokin matasa Mohammad Mehdi Tondgouyan ya shaida wa kamafanin dillacin labarai na IIna.

Ya yi gargaɗin cewa gaza magance matsalar babban ƙalubale ne.

‘Ba za mu haƙura ba’

Ko da yake suna sane da batun makomar yaran da aka haifa a tsarin na zaman dadiro, kaɗan ne daga cikin fitattun mutanen Iran suka fito suka yi magana game da batun.

Tsohuwar ƴar majalisa mai da’awar kawo sauyi Parvaneh Salahshouri ta taɓa magana a watan Satumban da ya gabata, lokacin da ta yi gargaɗin cewa zubar da ciki shi ne kawai zaɓi ga matan da suka yi ciki.

Amma Ms Salahshouri ta sha suka inda wasu suka bayyana kalamanta da “iƙirarin da ba ya da tushe”.

Wasu na ganin ƙalubalen tattalin arziki da kuma wasu al’adu kafin aure na ingiza ƴan Iran daga tsarin da ya dace aka amince da shi na aure.

Wasu har ana karfafa wa masu tasowa gwiwa kan tsarin, ta hanyar ba su tallafin da ba kuɗin ruwa.

“Wannan abin takaici ne”, in ji Shina ƴar shekara 31 daga garin Hamedan da ke yammaicn ƙasar.

“Yaya batun biyan hayar gida,” a cewarta tare da bayyana damuwa kan tsadar gidaje da kuma hauhawar farashi a shekarun baya.

Shina tsawon shekaru 10 ta shafe tare da saurayinta Sadegh, kuma ta ɗauki tarayyarsu a matsayin hanyar bijerewa hukumomin Iran.

“Ba mu yarda da wannan tsarin tilastawa ba na (aure),” in ji ta. Ta yaya saboda ƙin amincewa da wasu sharuɗɗa zai haramta tarayyarmu?”

Ana ganin wannan ba ɓoyayyen abu ba ne tsakanin ƴan Iran musamman a kafofin sada zumunta na intanet – kuma wata alama ce da ke nuna cewa tsangwama ta fara tafiya.

Manhajar Telegram ta kasance kafar da Iraniyawa ke neman masoya, ɗaya daga cikin shafin yana da sama da mabiya 45,000 waɗanda suka yaɗa bayanansu da nufin samun masoya.

Amma har yanzu makomar irin waɗannan mutanen na tsaka mai wuya musamman daga manyan masu tsattsauran ra’ayi masu adawa da tsarin.

‘An tarwatsa burinmu’

Ga Shina da Sadegh, matakan na yanzu suna da tasiri da tsada sosai.

Masoyan sun nemi biza a Jamus lokacin da Shina ta samu ciki a 2016, tare da sanin matsalolin shari’a da za su fuskanta da ɗansu. Amma an ki yarda da su.

“An twarwatsa burinmu kuma zubar da cikin ne kawai mafita,” kamar yadda Shina ta bayyana.

Iran ta haramta zubar da ciki har sai idan cikin na barazana ga lafiyar mace. Saboda wannan dokar, babu kwayoyin zubar da ciki a kasuwa, kuma yawancin mata ana tilasta masu amincewa da mummunan hanyar da aka haramta ta zubar da ciki da ke barazana ga lafiyarsu.

Wata ƴar shekara 36 da ta nemi a sakaya sunanta saboda dalilai na tsaro ta ce sau uku tana zubar da cikin da ta samu ta hanyar da ba ta dace ba a wata asibiti mai zaman kanta a Tehran.

Ga wasu, ficewa Iran wani zaɓi ne gare su.

Pari da saurayinta Yassin, waɗanda dukkaninsu ƴan shekara 35 ne sun kashe dukkaninsu kudinsu domin sayen gida a Istanbul na Turkiyya, birnin da ya kasance maɓuyar Iraniyawa saboda halin taɓarɓarewar tattalin arziki da kuma rashin samun walwala.

“Lokacin da na fara fahimtar ina da ciki na yanke shawarar cewa ba zan zubar ba a wannan karon, duk kuwa da abin da zai biyo baya,” in ji Pari, wacce ta taɓa zubar da ciki.

“Barin ƙasarmu ba ƙaramin abu ba ne. Amma za su yi renon ɗanmu cikin soyayya, kuma abin ya fi muhimmanci kenan,” a cewarta.

“Har yanzu, ba zan iya daina tunanin saduwa da abokai na ba, waɗanda ke burin samun haihuwa kuma an hana su samun damar.”

Labarai Makamanta