Yawaitar Satar Mutane: Kotun Duniya Za Ta Tuhumi Buhari

Karim Asad Ahmad Khan, mai gabatar da kara na kotun manyan laifuka ta duniya (ICC) na neman izinin gudanar da bincike kan sace -sace da garkuwa da mutane a Najeriya.

Binciken zai shafi sace -sacen mutane a Arewacin Najeriya, rufe makarantu, da gazawar gwamnatin tarayya da na jihohi wajen kawo karshen sace -sacen.

An fitar da wannan rahoton ne a ranar Lahadi Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama da Tattalin Arzikin Kasa (SERAP) ce ta fitar da shi.

A cikin takardar koke a watan Satumba, SERAP ta bukaci Khan da ya matsa kaimi don a gurfanar da wadanda ake zargi da hannu a aikata laifukan.

A cikin wasikar 22 ga Oktoba mai lamba. OTP-CR-363/21, Khan ya shaida wa SERAP cewa an cika sharuddan bincike kan jerin sace-sacen.

Wasikar wadda aka sanya mata hannu a madadin mai gabatar da kara ta hannun Mark P. Dillon, Shugaban Sashin Labarai da Sashen Shaida, ta ce binciken farko na karar ya kusa kammala.

Ta ce a karkashin layi na 53 na Dokar Rome, mataki na gaba a tsarin shari’ar “shine shirya shigar da bukatar zuwa gaban Kotun don neman izinin bude bincike kan Najeriya.

Wasikar ta kara da cewa “da zarar an shigar, za a gabatar da bukatar a bainar jama’a a gidan yanar gizon Kotun: www.icccpi.int.

A cikin wata sanarwa, SERAP ta jinjinawa mai gabatar da kara na ICC saboda daukar wani muhimmin mataki wajen tabbatar da cewa an fallasa mutanen da ke da alhakin ta’asar da ake yi wa yara ‘yan makaranta da sauran al’ummar Najeriya.

Kungiyar tace “wadanda wannan laifukan suka shafa sun cancanci a yi musu adalci. SERAP za ta yi aiki kafada da kafada da kotun duniya don cimma wadannan muhimman manufofi ”, in ji mataimakin daraktan ta, Kolawole Oluwadare.

Ko a makon da ya gabata ma dai wasu yan bindiga sun saki wasu ƙarin dalibai 27 da malamai 3 da aka sace daga Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Birnin Yauri a jihar Kebbi.

Daliban wadanda aka yi garkuwa da su daga jihar ta Kebbi sun kwashe tsawon watanni hudu tare da wadanda suka yi garkuwa da su, wasu kuma har yanzu ana tsare da su yayin da ake ci gaba da tattaunawa don sakin su.

Gwamna Atiku Bagudu ya fadawa wadanda abin ya shafa da su dauki satar daliban a matsayin fitina daga Allah.

“Ko Annabawan Allah, wadanda su ne mafifitan mutane kuma masu aminci, an jarabce su saboda a gwada su.

“Abu daya ne tabbatacce: idan aka gwada kuma kuka yi haƙuri, Aljanna ce makomar ku kuma Allah ne kaɗai ya san ladan ku”, in ji Gwamna Bagudu Na Kebbi.

Labarai Makamanta