Yau Take Sallah A Najeriya Da Saudiyya

Yau Alhamis 13 ga wata Mayun shekarar 2021 ita ce ta kasance ranar 01 ga watan Shawwal na shekarar 1442 bayan hijirar FIyayen talikai Annabi Muhammadu SAW daga Makka zuwa Madina wato ranar Sallah ƙarama a kasashen Najeriya da Saudiyya.

Tun da fari sai da fadar mai alfarma Sarkin Musulmi ta bada sanarwar duba jinjirin Wata a ranar Talata 29 ga Ramadan, inda sanarwar ta bayyana cewar idan ba a ga watan za’a cike Ramadan zuwa kwanaki 30 a ranar Laraba sannan ayi bukukuwan sallah a ranar Alhamis.

Rahotanni daga fadar mai alfarma Sarkin Musulmi sun tabbatar da cewar ba a samu damar ganin watan ba a ranar Talata wannan ya sanya aka cike azumin zuwa kwanaki 30 a ranar Laraba inda a yau ta kasance ranar ƙaramar Sallah.

A gefe guda ita ma ƙasa mai tsarki ƙasar Saudiyya ta tabbatar da rashin ganin Watan a ranar Talata wanda hakan ya sanya suma a ƙasar suka yi azumi na kwanaki 30 sannan suke gudanar da bukukuwan sallah a yau Alhamis.

Tuni gwamnatin tarayya ta bayar da hutun kwanaki biyu a Najeriya domin gudanar da bukukuwan sallah, tare da yin kira ga jama’ar Musulmi su yi amfani da lokutan bukukuwan sallan wajen sanya Najeriya cikin addu’o’i na fita daga halin da take ciki na matsalar tsaro.

Labarai Makamanta

Leave a Reply