Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar an tsaurara tsaro a jahoji 28 cikin jahohi 36 inda za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jahohi a yau Asabar.
Babban sifeton ‘yan sandan Najeriyar, Usman Baba, ya ayyana dokar hana zirga-zirgar ababen hawa a jihohi daga karshe 12 na tsakar daren Juma’a har zuwa karfe shida na yammacin ranar Asabar bayan kammala zaɓukan.
Rahotanni sun ce an samu hatsaniya a tsakanin magoya bayan jam’iyyu a Jihar Legas, inda gwamnan Jihar mai ci na jam’iyyar APC, Babajide Sanwo-Olu, yake fuskantar zazzafar adawa daga ɗan takarar gwamnan Jihar na jam’iyyar Labour, Gbadebo Rhodes-Vivour.
Jam’iyyar ta Labour ce dai ta samu kuri’u mafi yawa a zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana watan jiya a Jihar Legas.
Shugaban Hukumar zaɓe Farfesa Mahmoud Yakubu ya sanar da cewa Hukumar ta tanadi dukkanin abubuwan da ake buƙata domin tabbatar da samun nasara a yayin zaben.
You must log in to post a comment.