‘Yar Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ta Roki ‘Yan Najeriya Koda

Sonia, diyar sanata Ike Ekweremadu, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, ta roki jama’a da su taimaka mata da gudunmawar koda. Diyar dan majalisar ta yi wannan rokon ne a daidai lokacin da iyayenta suka shiga tsaka mai wuya a kokarinsu na ceto rayuwarta.

An kama Ekweremadu da matarsa a watan Yuni lokacin da suke kokarin samawa Sonia gudunmawar koda daga wani matashi a birnin Landan, an gurfanar da ma’auratan a gaban kotu kan zargin safarar mutum da kokarin cire wani sassa na jikin karamin yaro da bai balaga ba.

Daga bisani an bayar da belin Beatrice, matar dan majalisar yayin da shi kuma yake tsare har zuwa lokacin da za a sake zama kan shari’arsa a watan Oktoba.

A wata wallafa a shafin Instagram a ranar Litinin, Sonia, wacce ke zaune a UK, ta bukaci jama’a da su taimaka mata. Wani bangare na wallafar na cewa: “Ni Sonia Ekweremadu, ina rokon jama’a da su kawo mun dauki sannan su ceto rayuwata. Shekaruna 25 kuma na kammala karatun jarida a jami’ar Coventry.

Na dakatar da karatun digirina na biyu a jami’ar Newcastle a 2019 lokacin da aka gano ina dauke da cutar koda. “Iyayena na ta gwagwarmayar ceto rayuwata kuma sun kai ni asibitoci da dama, amma rashin lafiyan ya ci gaba kuma yana kara tabarbarewa. Ina raye a yau ne saboda ni’imar Ubangiji. Yanzu ina Landan, UK, ana yi mani wankin koda duk bayan awa 5 sau 3-4 a mako.

Labarai Makamanta