Yanzu Ne Ya Dace A Saki Zakzaky Da Zeenatu – Deji Adeyenju

“Abin burgewa ne da Shugaba Buhari ya bada dama tare da yin afuwa ga fursunoni guda 2,600 saboda gujewa yaduwar cutar Corona, tare da daukewa mutane kudin wuta na tsawon watanni biyu.

“Wannan shine lokacin da ya fi da cewa a saki Malam Zakzaky da Matar sa, yakamata a kawo karshen bakin cikin da ‘yan Shi’a suke fama da shi” Inji shi

Sama da shekaru 4 a na tsare da Malam Zakzaky cikin mawuyacin hali na rashin tabbas, mutane, kungiyoyi sun yi ta kira da a sake shi amma hukumomi sun yi burus, sun yi ta nuna hadarin dake cikin cigaba da tsare shi musamman a mummunan yanayin rashin lafiya da yake fama da ita, wasu lokutan hukumomin suna maida martani wasu lokutan kuma su yi shiru kamar ba su ji ba.

Tuni dai wata babban kotu a Abuja karkashin mai Shari’a Justice Kolawale ta yi umarnin da a sake Malamin tin shekarar 2016, amma hakan bai yiwu ba, inda hukumar Nijeriya ta ce ba ta ga dalili ba har ma tace ta daukaka kara. Hatta wadanda ake zargi da kisa da ake cewa umarnin Zakzaky ne tuni kotu ta wanke su ta sallame su sama da su 200.

Related posts