‘Yan Siyasa Na Da Hannu Dumu-Dumu A Matsalar Tsaro – Yero

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero, ya yi magana a game da halin rashin tsaro da ake fama da shi a Najeriya inda ya bada wasu shawarwari.

Mukhtar Ramalan Yero ya ke cewa abubuwa biyu ne su ka jefa kasar a halin da ta ke ciki, A na sa ra’ayin ba komai ba ne wadannan sai talauci da rashin shugabanci.

Alhaji Mukhtar Ramalan Yero ya nuna cewa muddin ba a fito an yi yaki da talauci da kuma bata-garin shugabanni ba, ba za a taba samun zaman lafiya a Najeriya ba.

Mukhtar Yero ya yi wannan jawabi ne a wajen wani taro da Makarantun NTIC watau Nigerian Tulip International Colleges da Ufuk Dialogue su ka shirya a jiya.

Dallatun Zazzau ya raba matsalolin shugabanci da ake fuskanta a Najeriya zuwa ga matsalar shugabanci a cikin al’umma, da dangi, sai kuma addini da siyasa.
Daily Trust ta rahoto tsohon gwamnan na Kaduna ya na cewa ‘Yan siyasa su na da na su matsalolin, domin da yawansu su na neman mulki ne idanunsu a rufe.

Bayan wasu ‘Yan siyasa sun samu mulki, sai su fuskanci kalubalen kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a ofis inji tsohon gwamnan na jam’iyyar PDP.

“Wasu ‘Yan takara su na neman mukami ko ta wani hali, ba su damuwa da yadda su ka samu mulkin, bayan sun samu abin da su ke so, sai su fara gamuwa da matsaloli.”
Yero ya ke cewa irin wannan ‘Yan siyasa su kan gamu da matsalar zama lafiya, sai su yi ta kokarin kawo gyara, alhalin su ne su ka fara jawo rashin tsaron.

Related posts